1 Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa,Mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.
2 Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba,Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.
3 Sa'ad da ban hurta zunubaina ba,Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.
4 Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji,Ƙarfina duka ya ƙare sarai,Kamar yadda laima yake bushewa,Saboda zafin bazara.
5 Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka,Ban ɓoye laifofina ba.Na ƙudurta in hurta su gare ka,Ka kuwa gafarta dukan laifofina.