1 Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa,Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa.
2 Domin yana ganin kansa shi wani abu ne,A tsammaninsa Allah ba zai tona asirinsa ba,Ya hukunta zunubinsa.
3 Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi,Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.
4 Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa,Halinsa ba shi da kyau,Ba ya ƙin abin da yake mugu.
5 Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,Ta kai har sammai,Amincinka ya kai sararin sammai.