9 Kai ne mafarin dukan rai,Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske,
10 Ka yi ta ƙaunar waɗanda suka san ka,Ka yi wa adalai alheri.
11 Kada ka bar masu girmankai su fāɗa mini,Kada ka bar mugaye su kore ni.
12 Dubi inda mugaye suka fāɗi!Can suka kwanta, ba su iya tashi.