1 Da kunnuwanmu muka ji, ya Allah,Kakanninmu suka faɗa mana,Manya manyan abubuwa da ka aikata a lokacinsu,A zamanin dā,
2 Yadda kai da kanka ka kori arna,Ka dasa jama'arka a ƙasarsu,Yadda ka hori sauran al'umma,Amma ka sa jama'arka su wadata.
3 Ba da takubansu suka ci ƙasar ba,Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba,Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka,Ta wurin tabbatar musu kana tare da su,Kana nuna musu kana ƙaunarsu.
4 “Ya Allah, kai ne Sarkina,Ka ba jama'arka nasara.
5 Da ikonka muka kori abokan gābanmu,Saboda kasancewarka tare da muMuka rinjayi magabtanmu.