2 Yadda kai da kanka ka kori arna,Ka dasa jama'arka a ƙasarsu,Yadda ka hori sauran al'umma,Amma ka sa jama'arka su wadata.
3 Ba da takubansu suka ci ƙasar ba,Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba,Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka,Ta wurin tabbatar musu kana tare da su,Kana nuna musu kana ƙaunarsu.
4 “Ya Allah, kai ne Sarkina,Ka ba jama'arka nasara.
5 Da ikonka muka kori abokan gābanmu,Saboda kasancewarka tare da muMuka rinjayi magabtanmu.
6 Ban dogara ga bakana ba,Takobina kuwa ba zai cece ni ba.
7 Amma ka cece mu daga abokan gābanmu,Ka kori waɗanda suke ƙinmu.
8 Za mu yabe ka kullum,Mu yi maka godiya har abada.”