2 Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,Kai mai kyakkyawan lafazi ne,Kullum Allah yakan sa maka albarka!
3 Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,Kai mai iko ne, Maɗaukaki!
4 Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,Domin ka tsare gaskiya da adalci.Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.
5 Kibanka suna da tsini,Suna huda zuciyar abokan gābanka,Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.
6 Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin!Kana mulkin mallakarka da adalci.
7 Kana ƙaunar abin da yake daidai,Kana ƙin abin da yake mugu.Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka,Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.
8 Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya,A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.