1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.
2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,Ko da duniya za ta girgiza,Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,
3 Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.
4 Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.
5 Allah yana zaune cikin birnin,Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.