2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,Ko da duniya za ta girgiza,Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,
3 Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.
4 Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.
5 Allah yana zaune cikin birnin,Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.
6 An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza,Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.
7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!
8 Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi!Dubi irin ayyukan al'ajabi da ya yi a duniya!