1 Ku yi tāfi saboda farin ciki,Ya ku jama'a duka!Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!
2 A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka,Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.
3 Ya ba mu nasara a bisa jama'o'i,Ya sa muka yi mulkin al'ummai,
4 Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune,Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama'arsaWadda yake ƙauna.
5 Allah ya hau kan kursiyinsa!Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni,Lokacin da Ubangiji yake hawa!