6 Ku raira yabbai ga Allah,Ku raira yabbai ga sarkinmu!
7 Allah sarki ne na duniya duka,Ku yabe shi da waƙoƙi!
8 Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki,Yana mulkin al'ummai,
9 Masu mulkin al'ummai suka tattaruTare da jama'ar Allah na Ibrahim.Allah shi ne garkuwar jarumawa,Yana mulkin duka!