4 Sarakuna suka tattaru,Suka zo Dutsen Sihiyona,
5 Da suka gan shi sai suka yi mamaki,Suka tsorata suka gudu.
6 Tsoro ya kama su suka razana,Kamar mace wadda take gab da haihuwa.
7 Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.
8 Mun ji labarin waɗannan al'amura,Yanzu kuwa mun gan suA birnin Allahnmu, Mai Runduna,Zai kiyaye birnin lafiya har abada.
9 A cikin Haikalinka, ya Allah,Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.
10 A ko'ina jama'a suna yabonka,Sunanka ya game duniya duka.Kana mulki da adalci.