1 Ku ji wannan, ko wannenku,Ku saurara jama'a duka na ko'ina,
2 Da manya da ƙanana duka ɗaya,Da attajirai da matalauta baki ɗaya.
3 Zan yi magana da hikima,Zan yi tunani mai ma'ana.
4 Zan mai da hankalina ga ka-cici-ka-cici,In bayyana ma'anarsa sa'ad da nake kaɗa molo.
5 Don me zan ji tsoro a lokacin hatsari,Sa'ad da mugaye suka kewaye ni,
6 Mutanen da suke dogara ga dukiyarsu,Waɗanda suke fariya saboda yawan wadatarsu?
7 Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba,Ba kuwa zai iya biyan kuɗin ransa ga Allah ba.