1 Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana,Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.
2 Allah yana haskakawa daga Sihiyona,Da cikar jamalin Sihiyona.
3 Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba,Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa,Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.
4 Ya kira sammai da duniya su zama shaidu,Su ga yadda yake shara'anta jama'arsa.
5 Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna,Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su,Ta wurin miƙa hadaya.”