4 Ya kira sammai da duniya su zama shaidu,Su ga yadda yake shara'anta jama'arsa.
5 Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna,Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su,Ta wurin miƙa hadaya.”
6 Sammai suna shelar adalcin Allah,Domin shi yake yin shari'a!
7 “Ku ji, ya ku jama'ata, zan kuwa yi magana,Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra'ila.Ni ne Allah, Allahnku.
8 Ban tsauta muku saboda hadayunku ba,Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.
9 Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,Ko awaki daga garkunanku.
10 Gama namomin jeji nawa ne,Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.