9 Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,Ko awaki daga garkunanku.
10 Gama namomin jeji nawa ne,Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.
11 Dukan tsuntsayen da suke tashi a sararin sama nawa ne,Da dukan masu rai da suke ƙasa.
12 “Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba,Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.
13 Nakan ci naman bijimai ne?Ko nakan sha jinin awaki?
14 Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.
15 Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo,Zan cece ku,Ku kuwa za ku yabe ni.”