12 Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.
13 Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,Za su kuwa komo wurinka.
14 Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.
15 Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,Zan kuwa yabe ka.
16 Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17 Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,Zuciya mai ladabi da biyayya,Ba za ka ƙi ba, ya Allah.
18 Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,Ka sāke gina garun Urushalima.