2 Ka wanke muguntata sarai,Ka tsarkake ni daga zunubina!
3 Na gane laifina,Kullum ina sane da zunubina.
4 Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa,Na kuwa aikata mugunta a gare ka.Daidai ne shari'ar da ka yi mini,Daidai ne ka hukunta ni.
5 Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni,Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.
6 Amintacciyar zuciya ita kake so,Ka cika tunanina da hikimarka.
7 Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka,Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.
8 Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.Ko da yake ka ragargaza ni,Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.