6 Amintacciyar zuciya ita kake so,Ka cika tunanina da hikimarka.
7 Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka,Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.
8 Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.Ko da yake ka ragargaza ni,Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.
9 Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,Ka shafe duk muguntata.
10 Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,Ka sa sabon halin biyayya a cikina.
11 Kada ka kore ni daga gabanka,Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.
12 Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.