1 Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah,Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!
2 Ka ji addu'ata, ya Allah,Ka saurari kalmomina!
3 Masu girmankai sun tasar mini,Mugaye suna nema su kashe ni,Mutanen da ba su kula da Allah ba.
4 Na sani Allah ne mai taimakona,Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!