4 Na sani Allah ne mai taimakona,Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!
5 Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu!Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.
6 Da murna zan miƙa maka hadaya,Zan yi maka godiya, ya Ubangiji,Domin kai mai alheri ne.
7 Ka cece ni daga dukan wahalaina,Na kuwa ga an kori maƙiyana.