2 Dukan yini maƙiyana suna tasar mini,Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.
3 Sa'ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki,A gare ka nake dogara.
4 Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa,Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba.Me mutum kawai zai yi mini?
5 Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini,A kan kowane abu da nake yi,Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!
6 Sukan taru a ɓoye,Suna kallon duk abin da nake yi.Suna sa zuciya za su iya kashe ni.
7 Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu,Da fushinka ka kori waɗannan mutane!
8 Ka san irin wahalar da nake sha,Kana riƙe da lissafin yawan hawayena.Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?