1 Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu,Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!
2 Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta.Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!
3 Ka sa jama'arka su sha wahala ƙwarai,Ka ba mu ruwan inabin da ya bugar da mu.
4 Ka ta da tuta ga masu tsoronka,Domin su juya su gudu daga abokin gāba.
5 Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.