1 Ga Allah kaɗai na dogara,Cetona daga gare shi yake fitowa.
2 Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,Shi ne kariyata,Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
3 Har yaushe dukanku za ku fāɗa wa wani don ku yi nasara da shi,Kamar rusasshen garu,Ko kuma dangar da ta fāɗi?
4 Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja,Kuna jin daɗin yin ƙarairayi.Kuna sa masa albarka,Amma a zuciyarku la'antarwa kuke yi.
5 Ga Allah kaɗai na dogara,A gare shi na sa zuciyata.
6 Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,Shi ne kariyata,Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.