1 Ya Allah, kai ne Allahna,Ina sa zuciya gare ka.Duk niyyata ta nemanka ce,Raina yana ƙishinka,Kamar bussasshiyar ƙasa,Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.
2 Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka,In dubi ɗaukakarka da darajarka.
3 Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa,Saboda wannan zan yabe ka.
4 Muddin raina, zan yi maka godiya,Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.