2 Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka,In dubi ɗaukakarka da darajarka.
3 Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa,Saboda wannan zan yabe ka.
4 Muddin raina, zan yi maka godiya,Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.
5 Raina zai yi liyafa, yă ƙoshi sosai,Ni kuwa zan raira waƙoƙin murna na yabo a gare ka.
6 Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai,Dare farai ina ta tunawa da kai,
7 Domin kai kake taimakona kullayaumin.Da murna, nake raira waƙa,A inuwar fikafikanka,
8 Raina yana manne maka,Ikonka yana riƙe da ni.