6 Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai,Dare farai ina ta tunawa da kai,
7 Domin kai kake taimakona kullayaumin.Da murna, nake raira waƙa,A inuwar fikafikanka,
8 Raina yana manne maka,Ikonka yana riƙe da ni.
9 Waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni,Za su gangara zuwa lahira,
10 Za a kashe su cikin yaƙi,Kyarketai kuwa za su cinye gawawwakinsu.