1 Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata!Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!
2 Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,Da iskancin mugayen mutane.
3 Sukan wasa harsunansu kamar takuba,Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
4 Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau,Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.