2 Ku raira waƙar darajar sunansa,Ku yabe shi da ɗaukaka!
3 Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawaSuna da banmamaki ƙwarai!Ikonka yana da girma ƙwarai,Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.
4 Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada,Yana raira maka waƙar yabbai,Yana raira yabbai ga sunanka.”
5 Zo, ka ga abin da Allah ya yi,Ayyukansa masu ban al'ajabiWaɗanda ya aikata ga mutane.
6 Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa,Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa.A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.
7 Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa,Yana duban al'ummai,Don kada 'yan tawaye su tayar masa!
8 Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al'ummai,Bari a ji yabon da kuke yi masa.