4 Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada,Yana raira maka waƙar yabbai,Yana raira yabbai ga sunanka.”
5 Zo, ka ga abin da Allah ya yi,Ayyukansa masu ban al'ajabiWaɗanda ya aikata ga mutane.
6 Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa,Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa.A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.
7 Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa,Yana duban al'ummai,Don kada 'yan tawaye su tayar masa!
8 Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al'ummai,Bari a ji yabon da kuke yi masa.
9 Shi ne yake rayar da mu,Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.
10 Ka jarraba mu, ya Allah,Kamar yadda ake tace azurfa da wuta,Haka nan ka jarraba mu.