7 Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa,Yana duban al'ummai,Don kada 'yan tawaye su tayar masa!
8 Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al'ummai,Bari a ji yabon da kuke yi masa.
9 Shi ne yake rayar da mu,Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.
10 Ka jarraba mu, ya Allah,Kamar yadda ake tace azurfa da wuta,Haka nan ka jarraba mu.
11 Ka bar mu muka fāɗa a tarko,Ka ɗora mana kaya masu nauyi.
12 Ka bar maƙiyanmu suka tattaka mu,Mun ratsa ta cikin wuta da rigyawa,Amma yanzu ka kawo mu a lafiyayyen wuri.
13 Zan kawo hadayun ƙonawa a ɗakinka,Zan miƙa maka abin da na alkawarta.