5 Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa,Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye,Wato matan da mazansu suka mutu.
6 Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki,Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi,Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.
7 Sa'ad da ka bi da jama'arka, ya Allah,Sa'ad da ka yi tafiya a hamada,
8 Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa,Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza,Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.
9 Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah,Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.
10 Jama'arka suka gina gidajensu a can,Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.
11 Ubangiji ya ba da umarni,Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,