7 Sa'ad da ka bi da jama'arka, ya Allah,Sa'ad da ka yi tafiya a hamada,
8 Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa,Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza,Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.
9 Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah,Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.
10 Jama'arka suka gina gidajensu a can,Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.
11 Ubangiji ya ba da umarni,Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,
12 “Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu!Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”
13 Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa,Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya.(Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)