25 Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu,Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!
26 Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta,Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.
27 Ka riɓaɓɓanya zunubansu,Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.
28 Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai,Kada a sa su a lissafin jama'arka.
29 Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala,Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!
30 Zan raira waƙar yabo ga Allah,Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,
31 Wannan zai daɗaɗa wa Ubangiji raiFiye da hadayar bijimi,Fiye da a ba shi bijimi bana bakwai.