1 Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka,Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata,
2 Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni,Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni,A can za su yayyage ni kamar zaki.
3 Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan,Wato idan na yi wa wani laifi,
4 Idan na ci amanar abokina,Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,