6 Ka tashi da fushinka, ya Ubangiji,Ka kuma tashi ka yi gāba da hasalar abokan gābana!Ka tashi, ka taimake ni, gama adalci kake so a yi.
7 Ka tattaro dukan kabilun da suke kewaye da kai,Ka yi mulki a kansu daga Sama.
8 Ya Ubangiji, kai ne alƙalin dukan mutane.Ka shara'anta mini bisa ga adalcina,Gama ba ni da laifi, ina kuma da kirki.
9 Ka tsai da muguntar mugaye,Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki.Kai Allah mai adalci ne,Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.
10 Allah ne mai kiyaye ni,Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.
11 Allah alƙali ne mai adalci,Kullum kuwa yana kā da mugaye.
12 Idan mutane ba su tuba ba,Allah zai wasa takobinsa,