3 Ka zama mini lafiyayyiyar mafaka,Da kagara mai ƙarfi, domin ka tsare ni,Kai ne mafakata da kāriyata.
4 Ya Allahna, ka cece ni daga mugaye,Daga ikon mugga, wato mugayen mutane.
5 Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya,Tun ina yaro, nake dogara gare ka.
6 A duk kwanakina a gare ka nake dogara,Kana kiyaye ni tun da aka haife ni,Kullayaumi zan yabe ka!
7 Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa,Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.
8 Ina yabonka dukan yini,Ina shelar darajarka.
9 Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni,Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!