5 Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya,Tun ina yaro, nake dogara gare ka.
6 A duk kwanakina a gare ka nake dogara,Kana kiyaye ni tun da aka haife ni,Kullayaumi zan yabe ka!
7 Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa,Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.
8 Ina yabonka dukan yini,Ina shelar darajarka.
9 Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni,Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!
10 Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni,Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.
11 Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi,Gama ba wanda zai cece shi!”