1 Ka koya wa sarki ya yi shari'aDa adalcinka, ya Allah,Ka kuma ba shi shari'arka,
2 Don ya yi mulkin jama'arka bisa kan shari'a,Ya kuma bi da mulki da adalci.
3 Ka sa ƙasar ta mori wadatarta,Ka sa al'ummar ta san adalci.
4 Ka sa sarki ya yi wa talakawa shari'ar gaskiya,Ya taimaki waɗanda suke da bukata,Ya kuma hukunta azzalumai!
5 Ka sa su girmama kaMuddin rana tana haskakawa,Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.
6 Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki,Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.