4 Ka sa sarki ya yi wa talakawa shari'ar gaskiya,Ya taimaki waɗanda suke da bukata,Ya kuma hukunta azzalumai!
5 Ka sa su girmama kaMuddin rana tana haskakawa,Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.
6 Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki,Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.
7 Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa,Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.
8 Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku,Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.
9 Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa,Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.
10 Sarakunan Esbanya da na tsibirai,Za su ba shi kyautai,Sarakunan Arabiya da na HabashaZa su kawo masa kyautai.