8 Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku,Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.
9 Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa,Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.
10 Sarakunan Esbanya da na tsibirai,Za su ba shi kyautai,Sarakunan Arabiya da na HabashaZa su kawo masa kyautai.
11 Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa,Dukan sauran al'umma za su bauta masa!
12 Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi,Da waɗanda suke da bukata,Da waɗanda ba a kula da su.
13 Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta,Yakan ceci rayukan waɗanda suke da bukata.
14 Yakan cece su daga zalunci da kama-karya,Rayukansu suna da daraja a gare shi.