1 Hakika, Allah yana yi wa Isra'ila alheri,Da waɗanda suke da tsarkin zuciya!
2 Amma ina gab da fāɗuwa,Ƙafafuna sun kusa zamewa,
3 Saboda na ji kishin masu girmankai,Sa'ad da na ga mugaye suna arziki.
4 Ba su jin zafin ciwo,Su ƙarfafa ne, lafiyayyu.