16 Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan,Ko da yake ya cika wuya,
17 Sai sa'ad da na shiga Haikalinka,Sa'an nan na fahimci abin da zai sami mugaye.
18 Hakika ka sa su a wurare masu santsi,Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!
19 Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,Suka yi mummunan ƙarshe!
20 Ya Ubangiji, kamar mafarki sukeWanda akan manta da shi da safe,Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.
21 Sa'ad da zuciyata ta ɓaci,Hankalina ya tashi,
22 Sai na zama wawa, ban fahimta ba,Na nuna halin dabba a gabanka.