18 Hakika ka sa su a wurare masu santsi,Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!
19 Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,Suka yi mummunan ƙarshe!
20 Ya Ubangiji, kamar mafarki sukeWanda akan manta da shi da safe,Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.
21 Sa'ad da zuciyata ta ɓaci,Hankalina ya tashi,
22 Sai na zama wawa, ban fahimta ba,Na nuna halin dabba a gabanka.
23 Duk da haka ina tare da kai kullayaumin,Kana riƙe da hannuna.
24 Shawararka, tana bi da ni,Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.