21 Sa'ad da zuciyata ta ɓaci,Hankalina ya tashi,
22 Sai na zama wawa, ban fahimta ba,Na nuna halin dabba a gabanka.
23 Duk da haka ina tare da kai kullayaumin,Kana riƙe da hannuna.
24 Shawararka, tana bi da ni,Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.
25 In banda kai, wa nake da shi a Sama?Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya?
26 Kwanyata da jikina za su raunana,Amma Allah ne ƙarfina,Shi nake so har abada!
27 Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu,Za ka hallakar da marasa aminci gare ka.