20 Ka tuna da alkawarin da ka yi mana,Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!
21 Kada ka bari a kori waɗanda ake zalunta,Amma bari matalauta da masu mayata su yabe ka.
22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre kanka!Ka tuna fa, marasa tsoronka suna ta yi maka ba'a dukan yini!
23 Kada ka manta da hargowar maƙiyanka,Kada ka manta da hayaniyar da magabtanka suke ta yi.