8 Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.
9 Ba sauran tsarkakan alamu,Ba sauran annabawan da suka ragu,Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.
10 Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a?Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?
11 Me ya sa ka ƙi taimakonmu?Ka tasar musu ka hallaka su!
12 Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,Ka yi nasara da duniya.
13 Da ƙarfin ikonka ka raba teku,Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,
14 Ka ragargaje kawunan kadduna,Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.