1 Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka!Muna shelar sunanka mai girma,Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!
2 “Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah,“Zan kuwa yi shari'ar gaskiya.
3 Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace,Zan ƙarfafa harsashin gininta.
4 Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama,Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya,