1 Allah sananne ne a Yahuza,Mashahuri ne kuma a Isra'ila.
2 Wurin zamansa yana Urushalima,A dutsen Sihiyona zatinsa yake.
3 A can yake kakkarya kiban abokan gāba,Da garkuwoyinsu, da takubansu, i, har da dukan makamansu.
4 Ina misalin darajarka, ya Allah!Ina misalin ɗaukakarka a sa'ad da ka komo daga kan duwatsu,Daga korar abokan gābanka!