15 Ta wurin ikonka ka fanshi jama'arka,Zuriyar Yakubu da ta Yusufu.
16 Ya Allah, sa'ad da ruwaye suka gan ka, sai su tsorata,Zurfafan teku kuma suka yi rawar jiki.
17 Gizagizai suka zubo da ruwa,Aka buga tsawa daga sama,Aka kuwa yi walƙiya ko'ina.
18 Bugawar tsawarka ta gama ko'ina,Hasken walƙiya ya haskaka dukan duniya,Duniya ta yi rawa, ta girgiza, ta kaɗu.
19 Ka yi tafiya a teku,Ka haye teku mai zurfi,Amma ba a ga shaida inda ka taka ba.
20 Ka bi da jama'arka yadda makiyayi yake yi,Musa da Haruna suke lura da su.