5 Na yi tunanin kwanakin da suka wuce,Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.
6 Dare farai ina ta tunani mai zurfi,A cikin tunani nakan yi wa kaina tambaya.
7 A kullum ne Ubangiji zai yashe ni?Ba kuma zai ƙara yin murna da ni ba?
8 Ya daina ƙaunata ke nan?Alkawarinsa ba shi da wani amfani?
9 Allah ya manta da yin jinƙai ne?Fushinsa ya maye matsayin juyayinsa ne?
10 Sa'an nan sai na ce, “Abin da ya fi mini zafi duka,Shi ne ikon Maɗaukaki ya ragu.”
11 Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji,Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā.